Jarumar fim tayi hatsarin mota
Yadda yan mata ke daukar selfie(hoto da kanka) yayi yawa, yawancin yan matan suna saka kansu a hatsari a dalilin daukar hoto dan a saka abunda suke ciki a dandalin sadarwa.
Abunda mutum ya kamata ya fara kula da shi a rayuwar shi shine kiyaye lafiyar shi, in baka yi haka ba, to hoton da kake kokarin ka dauka kila ba zaka samu ganin shi ba.
Akwai yawancin mata da yawa a duniyan nan da basu damu da komai ba illa suga sunyi kyau a hoto, wadan nan ne yan matan da basu da wani aiki sai daukar hoto a guri mai kyau, ko wani sabon wuri da ya burge su.
KU KARANTA:
A yayin da take daukar selfie a kan hanya, bata kula da zuwan mashin mai kafa 3 ba (keke napep), sai dai taji tayi karo da ita, ta fadi kasa warwas.
Amma duk da hadarin da tayi, be hana ta cigaba da daukar hoton ba dan sanar da masu bin ta a dandalin sadarwa.
Wannan itace tabi'ar da yawancin mutane keyi, a maimakon a taimaka ma mutum in yayi hatsari, sai kaga ana ta daukar hoto dan fada ma mabiyan dandalin sadarwa.
Ku biyo mu a shafin mu na tuita @naijcomhausa.
Asali: Legit.ng