Liitan bogi, daya samu nasarar tiyata sau 8

Liitan bogi, daya samu nasarar tiyata sau 8

Hukumomi a kasar Kenya sun cakfe wani mutum da ake zargi likitane amma fan a bogi.

Liitan bogi, daya samu nasarar tiyata sau 8
Likitan Bogi Melly

Rahotanni sun shaida cewa, likitan mai suna Ronald Melly ya samu nasarar fede mutane, wato tiyata har sau 8 kafin ya shiga hannu.

Rahotan ya cigaba da bayyana cewar cikin mutane 9 da Melly ya yi ma tiyata a tsakanin 5 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yulio na wannan shekarar, mutum daya ne kawai ya rasu, inda sauran 8 din suka samu lafiya. Ita ma dayar data rasu dama tana cikin tsaka mai wuya ne koda aka kawo ta wurin likitan.

KU KARANTA: Kotu ta bada Bala Muhammed beli

Liitan bogi, daya samu nasarar tiyata sau 8
Medical team performing surgery

Sakamakon kwarewar Melly ya sanya wasu al’ummar kasar Kenya suke yin kira ga Gwamnati cewa ba daure Melly ya kamata ta yi ba, inda suka bada shawarar kamata yayi ta kais hi makaranta don kara samun horo, daga nan sai a bashi takardan izinin aikin likitanci.

Haka ma an kama wani yaro mai shekaru 18 kimanin sati biyu da suka gabata da laifin yin sojan gonan likita.

Jama’a mai kuke gani, a horar dashi ko a daure shi? Zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng