Ana gwajin sabon rigakafin kanjamau a Afrika ta kudu

Ana gwajin sabon rigakafin kanjamau a Afrika ta kudu

Kasar Afirka ta kudu ta fara wani gagarumin gwajin rigakafin yaki da cutar kanjamau ko Sida wanda masana kimiya ke fatar ganin shi ne na karshe wajen gano maganin cutar da ta kashe miliyoyin jama’a.

Ana gwajin sabon rigakafin kanjamau a Afrika ta kudu
HIV-protest

Bayan kwashe shekaru sama da 30 ana neman maganin cutar ta kanjamau ko Sida da aka yi wa la’kabi da lahira kusa ko Kabari Salamu Alaikum, a karon farko bayan gano cutar a shekarar 1983, masana kimiya na tunanin cewar hakarsu ta cimma ruwa.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Borno ya karyata Buhari?

Gwajin masanan da ake kira HVTN 702 zai shafi mutane sama 5,400 majiya karfi da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 35 a Yankuna 15 na Afirka ta kudu a cikin shekaru 4 masu zuwa.

Wannan kuma shi ne zai zama gwajin maganin cutar mafi girma da aka taba yi a duniya wanda ya farfado da kwarin gwuiwar masana kiwon lafiya da ke raba dare wajen nemo maganin.

Anthony Fuchi, Daraktan Cibiyar yaki da cututtuka na Amurka ya ce muddin aka samu nasarar gwajin, maganin zai taimaka sosai wajen kawo karshen mutuwar mutanen da ake samu.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: