Wasu hadurran jirgi dauke da yan was 7

Wasu hadurran jirgi dauke da yan was 7

- Shugaban kasar Brazil Michel Temer ya sanar da fara zaman makoki na kwanaki uku bayan hadarin jirgin da ya hallaka mutane sama da 70 ciki har da ‘Yan kungiyar kwallon kafar kasar.

- Cikin wadanda suka aike da sakon ta’aziyar su har da shahararrun ‘yan wasan kwallon kafa Pele da Maradona da Lionel Messi da kuma Paparoma Francis.

Wasu hadurran jirgi dauke da yan was 7
jirgin sama dauke da yan wasan brazil ya fadi

Wannan dai ba shi ne hadarin jirgin sama na farko ba da ke hallaka ‘yan wasa.

(1) A shekarar 1949 wani jirgi mai dauke da tawagar kungiyar kwallon kafar Torino Grande ta Italia ya fadi lokacin da ya bar kasar Portugal inda ya kashe mutane 31.

(2) A shekarar 1958, jirgin da ke dauke da ‘yan wasan kungiyar Manchester United ya fadi bayan ya sha mai a birnin Munich na Jamus , inda ya kashe mutane 23.

KU KARANTA: Arewa ta kusa samun tashar jiragen ruwan ta

(3) A shekarar 1961, kungiyar ‘yan wasan Amurka sun yi hadari a wani jirgi da ya fadi a Belguim, bayan wani wasan da suka yi da kasar Czechoslovakia inda ‘yan wasa 18 suka mutu.

(4) A shekarar 1972, kungiyar ‘yan wasan zari ruga ta Uruguay 40 sun mutu lokacin da jirgin su ya fadi akan hanyar zuwa Chile. Mutane 27 suka mutu nan take, kana 11 suka mutu daga baya.

(5) A shekarar 1987 wani jirgin Peru mai dauke da mutane 43 cikin su har da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar Alianza Lima, sun fada teku a Lima inda suka mutu.

(6) A shekarar 1994 daukacin ‘yan wasan kwallon kasar Zambia sun mutu a wani hadarin jirgin sama, sai Kalusha Bwalya ka dai ya tsira shi da baya cikin jirgin.

(7) A shekarar 2011 daukacin ‘yan wasan kungiyar kwallon gora na kankara na kasar Rasha 44 suka mutu akan hanyar su ta zuwa Minsk.

A cikin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin jirgin akwai 'yan jaridu da ma'aikatan jirgin da kuma tawagar Kulob din 'yan wasan kwallon kafar Chapecoense.

Jirgin ya fadi ne daf da filin saukar jiragen sama na Medellin da ke kasar Colombia.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: