Wani mutum ya kera mota mai tafiya a ruwa da kan hanya
Wani dan Najeriya yayi kira mai kayatar wa wadda ya sa kirar ta yadu a dandalin sadarwa da kuma ya kera mota da ba a kasa kawai take tafiya ba, tana tafiya har kan ruwa.
Hoton wannan abun hawar da yayi mai iyayin wadan nana ababen ya kawo tsokaci da yawa a dandalin sadarwa wanda da yawa suke ta yabawa basirar shi.
Yawancin wadanda suka yi tsokaci a dandalin sadarwa suna cewa ne ba abunda mutumin yake bukata illa taimako daga gwamnati da sauran kungiyoyin hadin kai dan ya kirkira abunda yafi wannan wata rana.
Yana nuna abunda ya kirkira na mamaki da yadda ake amfani da shi.
KU KARANTA:
Zamu iya ganin hoton mutumin yana bayyana ma wasu mutane abin da ya kirkira.
Da fatar wannan mutumin ze samu taimakon gwamnati dan mu samu yayi wani abun da ze fi wannan, kar ya zama cikin wadanda za'a manta da su.
Ku biyo mu a shafin mu na tuita@naijcomhausa
Asali: Legit.ng