Za'a gina tashar jiragen ruwa a Arewacin Najeriya

Za'a gina tashar jiragen ruwa a Arewacin Najeriya

- Gwamnatin jahar Borno zata kafa sabuwar tashar jirgin ruwa a garin Maiduguri, don rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta

- Shugaban hukumar kamfanin jirgin ruwa da ake kira Shippers Council Alhaji Hassan Bello, shine ya shaidawa manema labarai cewa zasu kafa tashar ne domin samar da ayyukan yi ga matasa kimanin 5000, wanda zai rage matsalolin rashin ayyukan yi da ake fama da shi

Za'a gina tashar jiragen ruwa a Arewacin Najeriya
Stacked Up Shipping Containers

KU KARANTA: Majalisar dokokin jihar nan tayi wani muhimmin zama kan luwadi

Da yake yiwa wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, karin bayani yace za a kafa tashar jirgin ruwan ne ta yadda za rika dauko madukin kayannan da ake kira container daga tashoshin Port Harcourt da Lagos ba tare da an bude su ba. wanda hakan zai taimaka wajen isar da kayayyakin da ake shigowa da su da zummar daukar su zuwa yankin jahar Borno da makwabta.

Kamar sauran tashoshin jiragen ruwa wanann tasha zata kasance babu banbanci, domin duk hukumomin dake a sauran tashohin jiragen ruwa zasu kasance a tashar, domin kawowa mutane sauki. Maiduguri dai ta kasance cibiyar ciniki, domin akan kai kaya kasashen daban daban da suka hada da Afirka ta Tsakiya da Chadi da Kamaru da Sudan da kuma Libiya.

Za dai a bude wannan tasha ne a garin Kwandiga, inda za ayi amfani da jiragen kasa da kuma manyan motoci wajen dakon kaya zuwa sabuwar tashar.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: