Jirgin sama dauke da ‘yan wasan Brazil ya fadi a Colombia

Jirgin sama dauke da ‘yan wasan Brazil ya fadi a Colombia

Wani jirgin sama dake dauke da ‘yan wasan wata kungiya kwallon kafa ta Brazil Chapecoense ya fadi a Columbia, BBC ta rahoto.

A cewar rahotannin, jirgin sama zai kai tawagar filin jirgin Madellin lokacin da ya bace zuwa radar.

Jirgin sama dauke da ‘yan wasan Brazil ya fadi a Colombia
Jirgin dake dauke da yan wasan kungiyar Chapocoense zuwa filin jirgin Madellin lokacin da ya fadi

An tattaro cewa jirgin na dauke da pasinjoji 72 daga kungiyar kwallon kafar Chapecoense tare da wasu ma’aikatan jirgi guda tara a ciki.

Amma an rahoto cewa hatsarin ya afku ne sakamakon rashin mai da misalign karfe 10.15 na dare agogon gida.

Kimanin mutane 10 ne suka ji rauni an kuma fidda su daga gurin da abun ya afku, shugaban hukumar La Union fire ya bayyana.

‘Yan wasan kungiyar Chapecoense Real na kan hanya ne domin buga wasa da Atletico Nacional ta Colombia a ranar Laraba.

Ya zuwa yanzu dai babu cikkaken bayani kan makomar yan wasan da ke cikin jirgin da kuma masu horar da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel