Dangote zai gina kamfanin casar shinkafa a Kano
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya tabbatar da cewa zai gina kamfanin casar shinkafa a Kano wanda zai rika amfani da shi wajen cashe shinkafar da ya noma a gonakinsa da ke jihohin Zamfara, Jigawa da Sokoto.
Haka ma, Attajirin ya bayar da sanarwar cewa zai kaddamar da kamfanin yin takin zamani a shekara mai zuwa wanda shi ne mafi girma a nahiyar Afrika kuma zai rika samar da tan 2.8 milyan na takin zamani a kowace shekara.
A satin da ya gabata ne dai Gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejenniya da kamfanin Dangote domin gina hanyar kankare mai nisan kilomita 42 daga garin Obajana zuwa Kabba a jihar Kogi.
KU KARANTA: An tura dubban sojoji Zamfara samar da tsaro
Kamfanin na Dangote zai kashe kimanin Naira biliyan 11 da rabi a aikin, amma an ba shi aikin ne a madadin biyan kudin haraji na sama da Naira biliyan biyar.
A yammacin jiya ranar Talata ne 22 da ga watan Nuwamba bangarorin biyu suka sanya hannu kan kwangilar a Abuja.
Babban sakatare a ma'aikatar ayyuka da gidaje da wutar lantarki Injiniya Magaji Abdullahi Gusau ne ya rattaba hannu a madadin gwamnatin tarayyar.
Yayin da mai bai wa shugaban kamfanin na Dangote shawara Injiniya Joseph Makoju ya sa hannu a madadin kamfanin, yana mai cewa, babban cigaba ne a tarihin Najeriya.
Kamfanin ya ce watanni 24 ne lokacin da aka amince kare kwangilar, amma ya ce ya kudiri aniyar kammala wa a cikin watanni 16.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng