Kungiyar Izala ta maida martani kan dokar wa'azi

Kungiyar Izala ta maida martani kan dokar wa'azi

- A Najeriya, wasu ƙungiyoyin addinin Musulunci a ƙasar, sun fara tsokaci game da shirin dokar ƙayyade wa'azi da wasu jihohin kasar ke shirin zartarwa

- Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'ah wa ikamatussunnah ta ce dokar ba za ta yi tasiri ba har sai an dorawa ƙungiyoyin addinin nauyin saka wa masu wa'azinsu ƙa'ida da kansu

Kungiyar Izala ta maida martani kan dokar wa'azi
A lokacin ziyarar kungiyar Izala a gidan Sheikh Isyaku Rabiu

Tun ba yau ba ne dai ake zargin masu wa'azin addini a kasar da cusa wa mabiyansu aƙidu masu tsauri ko kuma ingiza wutar rikici tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Hakan ya sa wasu jihohi suka fara yunkurin bullo da dokokin takaita ayyukan masu wa'azin.

KU KARANTA: An zargi Gwamnatin jihar nan da rufa-rufa wajen bada kwangila

A wani labarin kuma, cikin firar da yayi da majiyar mu tayi da gwamnan Kaduna ya bayyana cewa gwamnatinsa bata hana addinin Shi'a ba saboda gwamnati bata da ikon hana wani addini amma kungiyar El-Zakzaki ce ta haramta.

Duk wanda ya fito yace shi dan kungiyar El-Zakzaki ne to yayi laifi saboda gwamnati bata amince da kungiyar ba.

Dokar da jihar tayi anfani da ita ta samo asali ne tun 1963 lokacin Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto kuma firimiyan lardin arewacin Najeriya wanda shi ma yayi anfani da ita a duk lokacin da ake son tada zaune tsaye.

Jihar tayi dokar ne ba domin Shi'a ba saboda akwai wasu kungiyoyin Shi'a guda biyu kuma ba'a hanasu yin addininsu ba ama ba sa tare da El-Zakzaki. Gwamnatin Kaduna bata da wata matsala da wadannan kungiyoyin biyu. Gwamnati bata hanasu yin addininsu ba domin babu wata gwamnati da zata hana wani yin addininshi bisa ga dokar Najeriya.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng