Steven Gerrard yayi murabus daga wasan Ƙwallo

Steven Gerrard yayi murabus daga wasan Ƙwallo

Shahararren tsohon dan wasan kungiyar Liverpool Steven Gerrad yayi murabus daga taka tamola bayan kwashe shekaru 18 a harkar kwallon kafa.

Steven Gerrard yayi murabus daga wasan Ƙwallo

ɗan wasan ya samu nasarori da dama musamman a Liverpool inda ya kwashe yawancin shekarunsa yana taka leda, Gerrard ya fara wasa a Liverpool tun a shekarar 1998 a wasan da Liverpool ta gwabza da Blackburn Rovers.

Magoya bayan Liverpool ba zasu manta da rawar da Gerrard ya taka ba yayin da suka samu nasara a wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Turai na shekarar 2005 inda suka fafata da AC Milan a garin Istanbul.

KU KARANTA: Shahararrun yan wasa 4 da basu iya kwalliya ba (HOTUNA)

Gerrard mai shekaru 36 ya tashi daga Liverpool ne a shekarar 2015 bayan ya buga mata wasanni 504 inda yaci kwallye 120, daga nan ya koma LA Galaxy dake kasar Amurka inda ya buga wasanni 36 tare da zura kwallaye 5. Sa’annan Gerrard ya buga ma kasar Ingila wasanni 114 inda ya ci kwallaye 21.

Gerrard ya bayyana dalilinsa na ajiye kwallo kamar haka, “ba zan iya yin abin da nayi a baya ba, don haka ya zama wajibi na ajiye kwallo, sa’annan ina mika godiya ga duk wadanda suka taimaka min a nasarorin da na samu a Liverpool da LA Galaxy.”

Za'a iya bin labaran mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel