Gaskiya 9 game d Atiku Abubakar da ya kamata ku sani

Gaskiya 9 game d Atiku Abubakar da ya kamata ku sani

Tsohon mataimakin shugaban kasa Abubakar Atiku ya cika shekaru 70 a yau 25 ga watan Nuwamba, 2016.

A karkashin gwamnatin Olusegun Obasanjo an rantsar da Atiku a matsayin mataimakin shugaban kasa a mulkin damokradiyan Najeriya na biyu a ranar 29 ga watan Mayu na 1999, karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Duk da alaka mai karfi dake tsakaninsa da Obasanjo, kudirin Atiku na gudanar da kasar a matsayin shugaban kasa ya shahara da yi fice a siyasar Najeriya. Bayan harkan san a siyasa ga wasu abubuwa 9 masu ban al’ajabi game da wannan dan siyasar Najeriya rikita ka.

1. Abubakar yayi aiki a hukumar hana fasa kauri na Najeriya tsawon shekaru 20

Gaskiya 9 game d Atiku Abubakar da ya kamata ku sani

Bayan ya kammala karatu a 1969, lokacin yaki basasan Najeriya, hukumar hana fasa kaurin Najeriya wato Nigeria Custom Service sun dauke shi aiki.

2. An haifi Atiku Abubakar a cikin zuri’ar Fulani dan kasuwa kuma manomi Garba Abubakar

Gaskiya 9 game d Atiku Abubakar da ya kamata ku sani

Mahaifinsa da mahaifiyarsa, Aisha Kande, suna zaune a kauyen Jada; wanda a yanzu yake jihar Adamawa, ada jihar Gongola.

3. Atiku ne ya kafa intels, wani ma’aikatar mai wanda ke aiki a Najeriya da kasar waje

Gaskiya 9 game d Atiku Abubakar da ya kamata ku sani

Ya kuma kasance wanda ya kafa kungiyar Adama Beverages Limited, da kuma American University of Nigeria (AUN), wanda dukka ke a garin Yola.

KU KARANTA KUMA: Nasarori 7 da Atiku Abubakar ya samu

4. Atiku Abubakar ya kasance dan siyasar Najeriya, kuma dan kasuwa

Gaskiya 9 game d Atiku Abubakar da ya kamata ku sani

[caption id="attachment_1060801" align="alignnone" width="800"] Atiku Abubakar a lokacin yakin neman zabe[/caption]

Atiku ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasan Najeriya na biyu a mulkin damokradiya daga 1999 zuwa 2007. Yana da kwarewa a fannin siyasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Tare da Olusegun Obasanjo wanda ya kasance shugaban kasa.

Ya fara kasuwancinsa a lokacin kuriciya a matsayin jami’in kwastam. A 1974 ya nemi bashin naira dubu talatin da daya (31,000) don ya gina gidansa na farko a garin Yola, wanda ya zuba yan haya.

5. Yunkurinsa na shiga siyasa ya kasance a farkon 1980s amma farkon tsayawarsa takarar kujerar gwamna ya kasance a 1990.

Gaskiya 9 game d Atiku Abubakar da ya kamata ku sani

Ya nemi kuri’u a madadin yakin neman zaben gwamna na Bamanga Tukur, wanda ya kasance manajan daraktan hukumar jirgin saman Najeriya. Yayinda yayi takaran sa na farko a matsayin gwamna a jihar Gongola a 1990.

6. Atiku Abubakar ya tara matan aure da yawa saboda baida kani ko 'kanwa

Gaskiya 9 game d Atiku Abubakar da ya kamata ku sani

[caption id="attachment_1060814" align="alignnone" width="800"] Atiku Abubakar tarev da 'ya'yan sa[/caption]

Rasuwar yayarsa tun tana yar yarinya ya sa Atiku ya kasance da tilo a gurin iyayensa da suka rabu da juna. Kadaici ya sa shi auren mata da yawa. Ya ce: “bana so yaya na su kasance cikin kadaici kamar yanda ya kasance a baya.”

KU KARANTA KUMA: Atiku Abubakar ya bayyana yanda ya siya gida a shekara 14

7. Ya auri matarsa Titilayo Albert cikin sirri a 1971

Gaskiya 9 game d Atiku Abubakar da ya kamata ku sani

[caption id="attachment_1060827" align="alignnone" width="800"] Atiku Abubakar da matarsa Titi[/caption]

A shekaru 25 Atiku ya mari matarsa ta farko wacce ta kasance tana da shekaru 19 a Idi-Iroko, Lagas cikin sirri saboda yan uwansa basu yarda da tarayyan ba a farko.

8. Atiku ya haifi yarsa na fari yana da shekara 26

Gaskiya 9 game d Atiku Abubakar da ya kamata ku sani

A ranar 26 ga watan Oktoba 1972, Atiku ya zama uba lokacin da Titilayo ta haifi ya mace suka sanya mata Fatima.

9. Atiku ya kasance maraya

Gaskiya 9 game d Atiku Abubakar da ya kamata ku sani

[caption id="attachment_1060848" align="alignnone" width="800"] Atiku Abubakar[/caption]

Bayan rabuwar iyayensa, mahaifinsa ya rasu ta hanyar nutsewa a 1957. Ko da dai mahaifiyarsa ta kuma aure, ta rasu sakamakon ciwon zuciya a 1984.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng