Atiku Abubakar ya cika shekaru 70 a duniya
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya cika shekaru 70 da haihuwa
- Jam’iyyar APC ta taya Alhaji Atiku Abubakar murna, tace sune Najeriya da kuma tsohon mataimakin Shugaban Kasan yayi hidima wajen inganta rayuwa da siyasar al’umma
Tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya cika shekaru 70 a duniya, Jam’iyyar su ta APC ta taya sa murnar wannan rana. APC tace ba zai yiwu a rubuta Tarihin Najeriya ba tare da sunan Atiku ba.
APC tace Atiku Abubukar ya inganta rayuwar ‘Yan Kasar nan ta fannin mu’amala, zaman siyasa, tattalin arziki da cigaban al’umma. APC tace Atiku mutum ne wanda aba ruwan sa da bambancin kabila ko yare.
KU KARANTA: Obasanjo munafuki ne
A sakon taya Atiku Abubakar din murnar zagayowar Ranar haihuwar sa, Jam’iyyar APC ta roka masa karin shekaru cikin koshin lafiya da arziki, Shugaban Jam’iyyar ne dai ya aika da wannan sako. APC tace alherin Atiku ya taba kowa a Kasar nan
Haka kuma dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Atiku Abubakar din murnar zagayowar wannan rana ta haihuwar sa, Shugaba Buhari ya taya Atiku shigowa sahun ‘Yan Saba’una watau masu shekara 70 zuwa sama.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
https://youtu.be/wXmmTEAKDxo
Asali: Legit.ng