Shahararrun yan wasa 4 da basu iya kwalliya ba (HOTUNA)
Abinda da ban mamaki yadda wasu yan wasa ke nuna kwarewa a cikin fili, amma sai kaga sun kasa tabuka komai a fannin yin kwalliya da ado.
Legit.ng ta dauko muku wasu daga cikin wadannan gwanaye a harkar tamola, amma kasassu a bangare ado da kwalliya.
Shahararren dan kwallon Duniya dake rike da kambun gwarzon dan kwallo Lionel Messi ya fado cikin jerin wadannan yan wasa da basu iya ado ba, a iya cewa ma shine jagoransu.
Idan ba’a manta ba haka ya taba sanya wani wandon daya fi karfinsa a shekarar 2014 bayan kungiyar sat a Barcelona ta lallasa Real Madrid.
Haka ma aka hange shi sanye da gajeren wando yayin daya ziyarci shugaban kasa Gabon Ali Bongo a kasar sa.
KU KARANTA: Adebayor ya nuna tsadaddun abubuwan, hawanshi da gidan shi
Tsohon dan wasan Aresenal da Barcelona Alex Song dan kasar Kamaru shi ke biye da Messi a rukunin marasa iya wanka.
A shekarar 2015 ma wata jaridar kasar Ingila ta baiwa Alex lambar girmama ta marasa iya kwalliya.
Dan kasar Ingila Lenon ya sha bayyana tabbacin rashin iya wankansa tun ba yau ba.
Irin kwalliyan da Balotelli keyi abin dariya ne tamkar yadda yake rigima a filin kwallo.
Zaku iya samun mu a shafin sadarwa na Tuwita @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng