Kungiyar matsafa sun bayyana wanda zai lashe zaben Ondo

Kungiyar matsafa sun bayyana wanda zai lashe zaben Ondo

Yayin da zaben gwamnan jihar Ondo ke kara karatowa,wata kungiyar mayu da matsafan Najeriya tayi wani has ashen da ya sanya Yan Najeriya zuba ma sarautan Allah ido.

Kungiyar matsafa sun bayyana wanda zai lashe zaben Ondo

Kungiyar mayu da matsafa wato WITZAN reshen jihar Ondo tayi bayyana wanda zai lashe zaben gwamnan jihar Ondo da zai gudana a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba 2016 shi ne dan takarar jami’iyyar APC wato Rotimi Akeredolu.

Shugaba kungiyar WITZAN Dakta Okhue Iboi ne ya bayyana haka a karshen wani taron mayu da matsafa da suka gudanar a garin Ese Odon a jihar Ondo.

KU KARANTA: Yaro ďan shekara 3 ya ceci rayuwar mahaifinsa

Shugaban kungiyar ya yaba ma ýaýan kungiyar, inda yace suna da daman yin duka abinsa suke so matukar bai saɓa ma doka ba tunda dai Najeriya ba kasar wata addini bace. Shugaban ya koka da yadda yan Najeriya ke muzanta su a bainar jama’a, daga baya kuma su rugo wurinsu suna neman agaji.

Shugaban kungiyar mayu da matsafa (WITZAN) yace: “Za’a gwabza tsakanin APC,AD,PDP da SDP a zaben nan dake karatowa, amma dan takarar APC ne zai lashe zaben.”

Ya cigaba da fadin: “Abin da ban haushi yadda yan Najeriya ke nuna munafunci ƙarara. Misali da zarar sun ji labarin mayu da matsafa sai yi mana mummunar zato, amma su sani, kungiyar mu ta WITZAN kungiyace ta ýaýan alkhairi.

“Mutane sun manta da cewar ko a cikin littafin Injila akwai labarin Sarki Saul wanda ya taɓa neman shawarar wata matsafiya kafin ya tafi yaƙi, don ya sani ko zai samu nasara ko akasin haka. Sa’annan yace ai kasar Najeriya bat a musulmai bace ko na kirista kadai ba. Kasar Najeriya ta kowa ce.”

Za'a iya bin labaran mu a shafin ma na Tuwita @naijcomhausa

 

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel