Dara taci gida: Fasto mai mu’ijizar bogi ya hallaka wani

Dara taci gida: Fasto mai mu’ijizar bogi ya hallaka wani

Rahotanni na nuna cewa wanda wani fasto madamfari mai yin mu’ijizar bogi ya kira ruwa a birnin tarayyar Abuja a kwanakin baya.

Dara taci gida: Fasto mai mu’ijizar bogi ya hallaka wani

[caption id="attachment_1060882" align="alignnone" width="254"] Bishop Emmanuel Esezobor[/caption]

Game da cewan rahotanni, Faston mai suna , Bishop Emmanuel Esezobor, ya hada baki da wani dan kasuwa cewa zai bashi kudi N500,000 domin ya wayance cewa ya mutu sai shi faston ya tayar da shi. Ashe dubunshi ya cika yayinda mutumin ya mutu cikin makara kafin aka kaishi idan za’a tayar.

KU KARANTA:Tashin hankali a jihar Ondo: PDP tayi babban tuhuma

Karanta rahoton:

“Ga faston da baiwa dan kasuwa N500,000 domin hadin baki wajen mu’ijizar karya.

“Wani fasto ya baiwa dan kasuwa N500,000 domin yaudarar mutane cewa yam utu sai ya tayar da shi. Amma kafin su kai filin kwallon kafa inda ake tarn ,sai mutumi yam utu.

“Matar dan kasuwan ta kai kara ofishin yan sanda inda aka damke faston. Amma abin mamaki,an saki faston yanzu kuma yana cigaba da yaudarar mutane a cocinsa da ke Nyanya Abuja.

“Sunan faston , Bishop Emmanuel Esezobor, mai cocin Firehouse Church, a Nyanya.”

Ku biyo mu a shafinm na Tuwita: @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng