Yan wasan da suka samu nasarar shiga hazikan kungiyar UEFA
- 'Yan wasan Wales Joe Allen da Aaron Ramsey da Gareth Bale sun samu shiga jerin 'yan wasa 40 da za a zabi gwanayen tawagar 'yan wasan hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA na bana.
- Allen da Ramsey na daga 'yan wasan Premier 12 da ke cikin jerin sunayen wadanda aka zabo din.
Riyad Mahrez na kungiyar Leicester City da tsohon abokin wasansa N'Golo Kante dukkaninsu sun samu shiga sakamakon kofin Premier da suka dauka na shekarar da ta wuce.
Sauran 'yan wasan Premier da su ma suka samu shiga jerin sun hada da Toby Alderweireld da Laurent Koscielny da Paul Pogba da Kevin de Bruyne da Dimitri Payet da Sergio Aguero da Alexis Sanchez da Zlatan Ibrahimovic.
Zakarun Turai Real Madrid sun fi kowacce kungiya yawan 'yan wasa a cikin jerin inda suke da golansu Keylor Navas da 'yan wasan baya Sergio Ramos da Dani Carvajal da Pepe.
Sai kuma 'yan wasansu na tsakiya da suka hada da Luka Modric da Toni Kroos da 'yan wasan gaba Gareth Bale da Cristiano Ronaldo.
KU KARANTA: Rundunar sojoji ta kama wani sojan bogi
Barcelona tana da 'yan wasa biyar; Lionel Messi da Luis Suarez da Neymar da Andres Iniesta da kuma Gerard Pique.
Gaba dayan sunayen 'yan wasan 40 da za a fitar da 11 daga cikinsu sun kunshi masu tsaron raga, ko gololi hudu da 'yan baya 12 da 'yan wasan tsakiya 12 midfielders da kuma 'yan gaba 12.
Magoya baya za su kada kuri'ar zaben 'yan wasan ne na Uefa na shekara ta shafin intanet na hukumar ta Uefa, zuwa ranar uku ga watan Janairu.
Ga jerin sunayen 'yan wasan da kungiyoyinsu:
Gololi:Gianluigi Buffon (Juventus), Keylor Navas (Real Madrid), Jan Oblak (Atletico Madrid) Rui Patricio (Sporting Lisbon).
'yan wasan baya:Toby Alderweireld (Tottenham Hostspur) Jerome Boateng (Bayern Munich), Leonardo Bonnuci (Juventus), Dani Carvajal (Real Madrid), Diego Godin (Atletico Madrid), Raphael Guerreiro (Borussia Dortmund), Juanfran (Atletico Madrid), Joshua Kimmich (Bayern Munich), Laurent Koscielny (Arsenal), Pepe (Real Madrid), Gerard Pique (Barcelona), Sergio Ramos (Real Madrid).
'yan wasan tsakiya:Joe Allen (Stoke), Kevin De Bruyne (Man City), Yannick Carrasco (Atletico Madrid), Andres Iniesta (Barcelona), N'Golo Kante (Chelsea), Toni Kroos (Real Madrid), Grzegorz Krychowiak (PSG), Riyad Mahrez (Leicester), Luka Modric (Real Madrid), Dimitri Payet (West Ham), Paul Pogba (Man Utd), Aaron Ramsey (Arsenal).
'yan wasa gaba :Sergio Aguero (Man City), Pierre-Emerick Aubameyang (Borussia Dortmund), Gareth Bale (Real Madrid), Antoine Griezmann (Atletico Madrid), Gonzalo Higuain (Juventus), Zlatan Ibrahimovic (Man Utd), Robert Lewandowski (Bayern Munich), Lionel Messi (Barcelona), Neymar (Barcelona), Cristiano Ronaldo (Real Madrid), Alexis Sanchez (Arsenal), Luis Suarez (Barcelona).
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng