Yadda Jirgin kasa ya yi ajalin mutane 100 a India  (Hotuna)

Yadda Jirgin kasa ya yi ajalin mutane 100 a India (Hotuna)

- Wani jirgin kasa mau dauke da fasinja yayi hadarin a inda ya hallaka mutane 100 a yankin Utta Pradesh bayan da jirgin ya sauka daga kan layinsa

- Ma'aikatan ceto na ta kokarin kutsatwa cikin baraguzan jirgin don kaiwa ga mutanen da hadarin ya ritsa da su

 

Yadda Jirgin kasa ya yi ajalin mutane 100 a India  (Hotuna)
Jirgin da yayi hadari a India

Wani jirgin kasa ya goce daga kan layin dogo ya  kuma yi ajalin mutane 100, yayin da wasu kimanin  sama da 150 kuma su ka ji raunuka.

A cewar 'yan sanda, tarago-tarago 14 na jirgin kasan da ke tafiya garin Patna daga Indro ne suka goce  daga kan layin dogon da misalin karfe 03:00 na daren ranar Lahadi a agogon India, watau misalin karfe 12:30 kenan na ranar Asabar a Najeriya.

Yadda Jirgin kasa ya yi ajalin mutane 100 a India  (Hotuna)
wasu taragai na jirgin da suka goce daga layin dogo

Hadarin ya afku a kusa da birnin Kanpur na India, duk da cewa har yanzu ba san musabbabin hadarin ba, jaridar The Times of India, ta raiwaito wata an cewar, karyewar da layin dogon ne musabbabin hadarin. Ma'aikatan ceto na kokarin kai dauki don ceto wadanda su ka ji raunuka da kuma fito da gawawwaki daga tarago-taragon jirgin da su ka dai-dai-ce.

Yadda Jirgin kasa ya yi ajalin mutane 100 a India  (Hotuna)
Ma'aikata na kokarin ceto sauran wadandasuka makale a cikin taragan jirgin

A hirarta da BBC, daya daga cikin wadanda su ka tsira da rayukansu, Krishna Shave na cewa, "Wajen karfe ukun dare mu ka farka,  da muka ji tarago-tarago da yawa sun goje daga kan layinsu, kowa ya shiga dimuwa. Na ga gawawwaki da dama da masu raunuka da yawa. Yawancin mutanen da hadarin ya ritsa da su, su na kusa da taragon da ke kusa da injin da ya kife kuma sun ji munanan raunuka.”

KU KARANTA KUMA: Mutane 5 da ke da alhakin tabarbarewar Najeriya

Har ranar Lahadi da yamma ma'aikatan ceto su na ta amfani da manyan kayan aiki don su kai ga wadanda su ka tsira da ransu. Babban jami'in hukumar kula da jiragen kasa, Pratap Rai ya ce:

"Mu na amfani da duk wata dabara don mu ceto rayuka amma babballa taragon ba abu ne mai sauki ba. Kawo yanzu ma'aikatan ceto sun ceto wasu da su ka tsira da rayukansu, ciki har da kananan yara inda 'yan kallo su ka bige da shewa”.

Ministan al'amuran jiragen kasa na India, Suresh Prabhu an mai cewa, yana lura da halin da a ke ciki sosai. Ya kuma yi gargadi cewa za a dauki mafi tsaurin mataki kan wadanda su ka yi sanadiyyar afkuwar hadarin. Ya kara da cewa za a kaddamar da bincike nan take kuma za a biya diyya ga wadanda su ka mutu da wadanda suka jikkata.

Ku biyo mu a shafinmu na Tuwita a @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng