Kasar Saudiyya ta fara cika alkawarin biyar diyyar mamata

Kasar Saudiyya ta fara cika alkawarin biyar diyyar mamata

Hukumomin Kasar Saudiya tare da hadin gwiwar hukumar mahajjata ta Najeriya sun mikawa magadan Alhazai goma sha biyu na jihar Adamawa da suka rasa ransu a turairainiyar da ta abku lokacin akin hajjin 2015 kaddarorinsu.

Kasar Saudiyya ta fara cika alkawarin biyar diyyar mamata
Shugaba Buhari tare da sarkin Saudiya

Babban sakataren hukumar kula da jin dadin mahajjata na jihar Adamawa Injiniya Umaru Bobboi ya shaidawa majiyar mu cewa maido da kaddarorin wadanda suka rasun ya dauki tsawon lokaci ne saboda nazari mai zurfi da hukumomin suka yi wanjen tantance wadanda suka rasu da kuma magadansu.

Babban sakataren ya ce darasin da 'yan Najeriya musamman jami'an tsaro yakamata su yi koyi da shi shine na rikon amana da tsare gaskiya.

KU KARANTA: An gano wadda tafi kowa tsufa a Najeriya (Hotuna)

Cikin juyayi da tausayi daya daga cikin magadan Alhaji Lekki ya jinjinawa hukumomin Saudiya da na alhazan Najeriya da rikon amanar marayu.

Mutane dai na ganin cewa matakin na hukumomin Saudiyya suka dauka ya Kara kyakkawar gurbi dadai da koyarwar addinin Musulumci.

Bayaga mahajjata goma sha biyu da aka tantance gawarsu akwai mutane biyu da ba a ga gawarsu ba gamma aka bada tabbacin rasuwarsu bayan an dauki sanfarin jin in 'ya,yansu da name mahaifansu mata.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng