An kashe ‘Yan Boko Haram da dama

An kashe ‘Yan Boko Haram da dama

- Bayanai daga jaridar Premium Times na nuna cewa an kashe ‘yan Boko Haram fiye da 10

- An kara ne da ‘yan kungiyar Boko Haram da rundunar sojojin kasar Najeriya

- Sojojin Najeriya sun gano kasuwar ‘yan Boko Haram din da ke cikin Maiduguri

An kashe ‘Yan Boko Haram da dama
Mayakan Boko Haram

 

 

 

 

 

 

 

Rahotanni daga Jaridar Premium Times sun tabbatar da cewa an kashe mayakan Boko Haram guda 11 a Garin Borno. Rundunar Sojojin Kasar Najeriya ce dai ta samu galaba kan ‘Yan kungiyar na Boko Haram a karshen wannan makon.

Sojojin Kasar sun gano wata kasuwa da sansanin na ‘Yan Boko Haram da ke Garin Yale a Arewacin Borno. Nan fa aka gwabza inda aka kashe da dama, aka kuma yi rauni ga wasu. Rundunar Sojin Kasar na Bataliya ta 103 ta samu karbe makamai daga hannun ‘Yan ta’addan.

KU KARANTA: An rusa Makarantar shi'a a Zaria

Rundunar Bataliya ta 202 da 151 da kuma Rundunar CJTF suka taimaka wajen samun kai nasarar wannan hari. Sai dai bayan nan ‘Yan Boko Haram sun yi kokarin kai wani samame, amma dai Sojojin Kasar tuni suka farga. Har yanzu dai Hedikwatar Sojojin ba ta ce komai ba

Kwanakin baya dai daruruwan Mayakan na Boko Haram sun ajiye kayan yaki, sun ce ba su yi a Kasar Chad.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng