Kuma daina tunani zan dawo Inji Tsohon Shugaba Jonathan
- Jam'iyyar PDP ta tuna da Shugaba Jonathan, inda tace anyi Gwarzo
- Jiya Goodluck Jonathan ya cika shekaru 59 a duniya
- Jam’iyyar PDP tace Shugaba Buhari ba zai samu nasara wajen Yaki da cin hanci da rashawa a Kasar nan ba
Jam’iyyar PDP ta tuna da Tsohon Shugaba Jonathan Goodluck yayin da ya cika shekaru 59 a jiya. Shugaban Bangaren Jam’iyyar PDP din, Sanata Ahmad Makarfi yace Shugaba Jonathan din ba karamin jan gwarzo bane.
PDP tace har yanzu ana shan romon ayyukan da Shugaba Jonathan yayi wajen fannin tsarin mulki da siyasa, ilmi, da kuma sauran hanyoyin more rayuwa. PDP tace Shugaba Jonathan yana cikin wadanda suka mika mulki salin-alin a Nahiyar Afrika, ko don haka tauraruwar sa ta ke kara haske a duniya.
KU KARANTA: Shugaba Buhari bai biya Jonathan kudin sa ba na shekara guda
Ana ta rade-radin cewa Goodluck Jonathan din zai dawo, sai dai a shafin sa na kafar Facebook ya rubuta cewa shi fa ya tafi kenan, sai labari. Shugaba Jonathan yace ai yanzu mulki kuma sai ‘ya ‘yan su da jikoki, don su kam sun yi sun gama. Jonathan yace Kasa ai ba ta cigaba da Tsofaffi a mulki.
Haka kuma, Jam’iyyar PDP mai adawa a Kasar tace babu inda Shugaba Buhari zai kai wajen Yaki da cin hanci da rashawa a Kasar nan domin ya saka son kai a lamarin.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
https://youtu.be/wXmmTEAKDxo
Asali: Legit.ng