Manyan mutane 6 da ka iya kashe ka a Najeriya
Wani sabon rahoto ya sanya kasar Najeriya a matsayin kasa ta 3 da ke fama da ta’addanci a duniya, tare da tambayoyi game da lafiyar yan Najeriya.
Tsawon rai a Najeriya yayi karanci wanda ya mutane da dama cikin rudani, ga wasu yan Najeriya sannin cewa idan sun bar gidajensu ba lallai ne su dawo ba shine abunda ke faruwa a kullun.
Yan Najeriya na fama da wannan tsoron a kullun tare da burin cewa sa’a mai zuwa ba karshen su bane, wannan ya samo asali ne saboda wadannan mutane 6 nba iya kashe su.
1. Boko Haram
Ba tare da kokwanto ba, Boko Haram sun zamo ruwan dare, sakamakon hare-hare da dama da suka kai wa mutane wanda yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane yayinda suka mayar da wasu marasa galihu.
Ko da yake sojojin Najeriya sunyi yaki sosai don ganin sun magance su, amma duk da haka kungiyar yan ta’addan na ci gaba da kai hare-hare na rashin imani.
Harin yan kunar bakin wake na ci gaba a wasu yankuna cikin arewa maso gabas kuma mutane na tsoron cewa kungiyar zasu iya tayar dasu a ko wani lokaci.
KU KARANTA KUMA: Rancen $29.9b: Saraki ya maida martani ga Fayose, kafofin watsa labaru
2. Yan bindigan Niger Delta
A lokacin da yan kungiyar Boko Haram suka bar wasu yankuna na Arewa maso gabas cikin tashin hankali, yan bindiga a yankin kudu-maso-kudu sun sanya mutane da dama a yankin Niger Delta cikin tsoro da fargaba a kan rayuwarsu.
Yan bindigan a nasu tunanin wai suna yaki don dawo da yanci a yankin, a halin yanzu, ayyukansu ya kawo halaka mai girma ga mutanen Niger Delta. Saboda idan sojojin Najeriya suka zo kai hari, bay an bindigan abun ke shafa ba.
A wasu lokuta da dama ana kama mutunen da basu san haw aba ko kuma a kashe su a kokarin sojojin na ganin sun cimma yan bindigan. Haka kuma ayyuka irin su fashe-fashen bututunan main a barazana ga mutane, saboda ya na iya sanadiyar mutuwan mutane da dama.
3. Fulani makiyaya
Wannan kungiyar na sanya zuciyar al’umma cikin fargaba kamar yadda yan Najeriya basu san ainahin inda zasu ajiye sub a. a hare-haren da suke kaiwa a garuruwa daban-daban a fadin kasar, yan Najeriya da dama sun rasa rayukansu a hannun wadannan masu kisan.
4. Yan sanda
Ya kamata ace yan sanda sun kasance abokai, amma kididdiga ya nuna cewa yan sanda sunyi sanadiyar mutuwan yan Najeriya da dama, a a kwanakin nan.
Daga harbin ganganci a cunkoson jama’a, yan sandan Najeriya na saka mutane suji cewa basu tsira ba, kamar yadda yan Najeriya da dama basu yarda da hukuncinsu ba.
KU KARANTA KUMA: Atiku ya daura laifin kisan dan shekara 7 a kan tsarin shari’an Najeriya
5. Fusatattun masu zanga-Zanga
Daukar doka a hannu cikin jahilci na daya daga cikin abubuwan dake damun kasar Najeriya kuma a kullun yana dada tabarbarewa ne, idan aka zargi mutun a kan wani dan karamin laifi, hukuncin na iya kasancewa mutuwa.
Mutun zai yi mamaki ga yadda aka kashe wasu yan Najeriya da dama, sakamakon ayyukan yan zanga-zanga. Akwai misalai da dama da za’a iya duba, kuma ba’a yi komai da kawo karshen abun ba.
6. Masu tukin ganganci
Ana kawo rahoton hatsarurruka a kullun a fadin kasar nan, kuma tukin ganganci ke haddasa karo da dama wanda ke kai mutun kushewa tun kan lokaci.
Akwai masu tukin ganganci sosai a kwanakin nan, wasu da daman a tuki a halin maye koda kuwea a ce da rana ne zaka same su tatil cikin maye.
Canza akalar zance
Gaskiya ne kasar Najeriya na fuskantar matsalolin ta’addanci, da sauran abubuwan da ka iya zama barazana ga rayuwan yan Najeriya, duk da haka wadannan abubuwa na faruwa a sauran kasashe a fadin Afrika da ma duniya baki daya.
Don haka, bazamu ce halin da Najeriya ke ciki ya wuci gyara ba, har ila yau yanda ake rubuto abubuwa marasa dadi akan Najeriya ya kamata ya canja saboda yan Najeriya tsayyayu ne, kuma masu rayuwa mai kyau; ba dukkan abubuwan dake faruwa a Najeriya bane marasa kyau.
A karshe dole dukkanmu mu mutu, amma dai kawai buna burin ace mutuwarmu bai zo ta sanadiyar rikici ko mutuwar wulakanci ba.
Asali: Legit.ng