An kashe mugun maciji a jami'ar jihar Benue (hoto)
Hoton macijin ya bayyana bayan wasu dalibai masu bajinta sun kashe shi.
An kashe wani mugun maciji a makarantar koyon aikin likita ta jami'ar jihar Benie yayin da dalibai da malamai suka firgita.
Hoton macijin ya bayyana bayan wasu dalibai masu bajinta sun kashe shi kan hanyarsu ta zuwa aji.
KU KARANTA: Atiku ya maida martani ga kisan wulakanci da akayi wa dan shekara 7 a jihar Lagas
An samu bayanin cewa macijin bai yima kowa lahani ba duk ya yake mutane sun firgita.
Jami'oin Najeriya da yawa sun sha yin arangama da majizai a harabobin su. Mafi yawan jami'oin dake zagaye da dazuzzuka na fama da matsaloli irin wannan, wadansu sukan dauki matakan tsaro domin kiyaye kansu
Ka taba cin karo da mugun maciji?
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
Asali: Legit.ng