Gwamna Fayose ya karkatar da wasu kudi

Gwamna Fayose ya karkatar da wasu kudi

- Jam’iyyar APC ta jihar Ekiti tace Gwamna Ayo Fayose ya sha kwana da kudin biyan albashin ma’aikatan jihar

Mai magana da bakin APC yace Fayose ya karbo aron kudi daga gwamnati amma ya jefa aljihun sa

- Kakakin Jam’iyyar ta APC yace ya kamata majalisa ta sa ido ta ga inda Gwamna yake kai kudin

 

 

 

 

 

Kakakin Jam’iyyar APC mai adawa a Jihar Ekiti ya zargi Gwamnan Jihar Ayo Fayose da karkatar da wasu makudan kudi da ya karbo aro daga Gwamnatin Tarayya. Gwamnatin Tarayya ta ba Jihohi aron kudi domin su biya ma’aikatan su da ke bin bashi, sai dai wasu sun sha kwana ne kurum da kudin.

Gwamna Ayo Fayose yana kokarin hana Majalisar Dattawa binciken yadda yayi da na sa kudin da ya karba. Jam’iyyar APC tace Gwamna Fayose ya daina wasa da hankalin jama’a. Jam’iyyar tace ba shakka Gwamna Fayose ya jefa kudin da ya aro ne cikin aljihun sa.

KU KARANTA: Atiku makarayaci ne- El Rufai

Gwamnatin Jihar Ekiti dai tace babu wanda ya isa ya binciki yadda tayi da kudin ta, domin kuwa dokar Kasa ba ta bada wannan damar ba. Sai dai Sakataren yada bayanai na APC, Taiwo Olatunbsoun yace ba haka abin yake ba.

Haka kuma dai, ana shari’ar wani wai shi Abiodun Agebele na kusa da Ayo Fayose. Wanda ya bayyanawa Kotu cewa ya tura kudi da kan sa zuwa asusun Gwamna Ayo Fayose, wannan dai ana zargi yana daga cikin kudin makamai da aka raba lokacin zabe.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: