Matsafi ya tashi wani bayan ya caka masa wuka a wuya
Kunga wani abu daya faru yayin da matsafi ya tashi wani mutum bayan ya kashe shi ta hanyar caka masa wuka a bainar jama’a.
Kamar yadda zaku gani a faifan bidiyon, an nuna matsafin yana tsafi ne yayin daya caka ma wani mutum wuka a wuya, wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa. Sai dai nan da nan yayi wasu siddabaru sai ga mutumin nan ya tashi.
Matsafin ya daure gawar maamcin tare da rufe shi da farin zani, inda ya fara rawa yana zagaye gawar tare da furta kalaman siddabaru, daga nan sai jini ya fara bubbugowa daga sashin jikin mamacin da aka caka ma wuka, sai shugaban matsafan ya tinkari gawar inda nan ma yayi wasu siddabaru akanta.
KU KARANTA: Wasu yan Najeriya a Amurka
Bayan wasu yan dakikoki kadan sai gawar ta tashi, ya mike tsaye yayi tafiyarsa ba tare da wani ya rike shi ba.
Ana haka sai shugaban matsafan ya fara tika rawa rike da farin zanin da aka rufe mutumin da shi.
Ga Hotunan kamar haka:
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng