Yan Shi'a masu zanga-zanga a kano na dauke da makamai –IGP
- Inspekto-Janar na yan sanda, Idris Ibrahim, yace mutanensa basu da zabi da ya wuce bude wuta a kan masu zanga-zanga na kungiyar musulman Shia
- Idris yace yan sandan sun sha arangama da mazan masu makamai, wanda suka toshe manyan titian, suka hana sauran yan Najeriya amfani da hanyan
Inspekto-Janar na yan sandan Najeriya, Idris Ibrahim, yace mutanensa basu da zabi da ya wuce su bude wuta a kan kungiyar nan ta musulinci masu zanga-zanga wato Shi'a a kauyen Tamburawa kusa da hanyar Kano.
Mista Ibrahim yace wasu mambobin kungiyar na dauke da muggan makamai da bindigogi da sauran makamai masu hatsari.
KU KARANTA KUMA: Boko Haram sun kuma kashe wani kwamandan sojoji
Ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zanta tare da wasu manema labarai a karshen ranar tuna hukumomi tsaro na 2017 wanda akayi a fadar shugaban kasa, Abuja.
Idris yace yan sandan sun sha arangama da maza masu makamai, wanda suka toshe manyan tituna, suka hana sauran yan Najeriya samun damar amfani da hanyar.
IGP din ya yi watsi da zancen cewa masu zanga-zangar na da hakki a karkashin kundin tsarin mulki na yawo a ko ina, ya bayyana cewa toshe hanya baya daga cikin abunda za’a kira da yanci na yawo.
Ya kuma yarda cewan wannan ci gaban zai iya kawo harin yan Boko Haram, idan aka bari ba tare da an duba ba.
Asali: Legit.ng