Dasuki yace ba zai je Jana’iza ba, zai tsaya yayi addu'a

Dasuki yace ba zai je Jana’iza ba, zai tsaya yayi addu'a

- Gwamnati tayi wa Sambo Dasuki tayin zuwa jana’izar Mahaifin sa da ya rasu a jiya

- Sai dai Sambo Dasuki yace ba zai je ba Inji Ministan cikin Gida, Abdurrahman Dambazzau

- Alhaji Ibrahim Dasuki, Mahaifin Sambo Dasuki ya rasu ne shekaran jiya

Dasuki yace ba zai je Jana’iza ba, zai tsaya yayi addu'a

 

 

 

 

Ministan cikin gida na Najeriya, Janar Abdurrahman Dambazzau mai ritaya ya bayyana dalilin da ya hana Sambo Dasuki halartar jana’izar Mahaifin sa. An bizne Mahaifin Sambo Dasuki, Ibrahim Dasuki a jiya ne a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Ibrahim Dasuki wanda shine Sarkin Musulmi na 18 a Najeriya ya rasu shekaran jiya a Garin Abuja yana da shekaru 93 a duniya. An yi jana’izar sa a Jiya yayin da dan sa, Sambo Dasuki yake rufe lokacin.

KU KARANTA: Ya kamata a saji Dasuki-Babban Lauya

Wasu dai suna tunanin Shugaban Kasa ne ya hana sa zuwa jana’izar Mahaifin na sa. Sai dai Ministan Harkokin cikin Gida na Najeriya, Abdurrahman Dambazzau ya bayyana cewa an yi wa Sambo Dasuki tayin zuwa duba Baban na sa tun yana kwance, sai dai yace ba ya bukatan zuwa, don zai yi masa addu’a. Da ya rasu kuma, aka kara tuntuban sa, yace dai ba zai je ba.

Dasuki dai sun yi magana da Shugaban Hukumar DSS na Kasa, amma yace ba sai ya je ba. Ministan yace wannan shine abin da ya faru. Sambo Dasuki dai yana tsare tun bara, ana zargin sa da cin kudin makamai. Wani Babban Lauyan Kasar nan, Femi Falana yayi kira da Gwamnatin Tarayya da ta saki shi

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel