Matar jajirtaccen soja da ya rasu Abu Ali tayi alkawari

Matar jajirtaccen soja da ya rasu Abu Ali tayi alkawari

Samira Ali matar marigayi Lt.Kanal Abu Ali Muhammad wanda yan ta' addan Boko haram suka kashe tare da wasu sojoji ranar juma'a 4 ga watan Nuwamba tayi na kasar Najeriya alkawali game da 'yayan ta.

Matar jajirtaccen soja da ya rasu Abu Ali tayi alkawari

Jaridar Vanguard tayi rohoton cewa Samira matar marigayi Abu Ali jajirtaccen soja ta fada yayin da take ganawa da wata kungiya mai zaman kanta mai suna"Nigerian Fallen Heroes 2017 project " wato kungiyar tunawa da yan mazan jiya" a yayin da suka zo mata gaisuwa a gidan iyayen ta da ke Kaduna ranar lahadi 13 ga watan Nuwamba , cewa tayi alkawalin zata tada yaran ta jarumai kamar mahaifin su.

Matar jajirtaccen soja da ya rasu Abu Ali tayi alkawari

Tace wanda yara na sun riga sun san cewa baban su ya rasu, ina nufin manyan masu wayau. Abunda ya rage gare ni shine in yi kokarin tada su kamar yadda mahaifin su yayi burin yi, dan su zama kamar shi, su zama abunda kasar Najeriya zata yi alfahari da su.

Abun kaico ne ace ya barsu a kananan shekarun nan, amma zasu tuna kullum ubane mai kula da da kauna gare su kamar yadda yake yi man. Banda wani abu da zan kara cewa face ince na bar komai hannun Allah madaukakin sarki.

Jaridar Vanguard tayi rohoton cewa Ali Abu ya bar yaya 3 Fatima Ali yar shekara 7 , Muhammad Ali Abu shekara 4 da Yasmin Abu Ali yar shekara 1.

Sai dai munji cewa hedikwatar sojoji sun karyata cewa gwamnati ta ta biya kudi kafin a saki yan matan Chibok guda 21.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng