Labari mai ban tausayi na matar da ta auri saurayi mai cuta

Labari mai ban tausayi na matar da ta auri saurayi mai cuta

- Talatu John (sunan karya) ta auri saurayinta mai kanjamau kwanan nan

- Mutunen mai suna Emmanuel yasa mata cutar lokacin da suke nema

- Tayi shawarar aurensa domin tana sonsa

Labari mai ban tausayi na matar da ta auri saurayi mai cuta

Wata daliba mai karatun gaba da digiri na farko mai suna Talatu John (sunan karya) ta auri wani mutum mai suna Emmanuel wanda ya sa mata ciwon kanjamau. Sun fara soyayya bayan sun hadu a 2014.

KU KARANTA: ‘Yan fashi sun hallaka Manajan Banki da Kashiya a Ekiti

Matsalolinta sun fara a cikin Yuni 2016 bayan ta gane cewa ta kamu da kanjamau. Talatu tana gaya ma Punch cewa: "Abinda yayi mani ciwo shine saurayina nada cutar amma bai gaya mani ba domin muna saduwa maras kariya a kai a kai. Ina sonsa matuka, saboda son da Nike masa mun sadu lokutta da yawa ba tare da munyi amfani da kwaroron roba."

Ku biyo mu a shafin ta Tuwita: @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: