Muna bayan Atiku Abubakar - Mutanen Adamawa
– Mutanen Adamawa na kokarin tunzura Alhaji Atiku Abubakar ya tsaya takarar shugaban kasa
– Mutanen jihar Adamawa sun ce suna bayan Atiku Abubakar
– Magoya bayan Atiku Abubakar sun ce ya taka rawar gani lokacin yana Mataimakin Shugaban Kasa
Mutanen Adamawa sun ce su fa suna bayan Alhaji Atiku Abubakar idan zai tsaya takarar Shugaban Kasar nan. Gwamnatin Jihar tace tana bayan Atiku Abubakar dari-bisa-dari wajen ganin ya zama Shugaban Kasar Najeriya.
Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Adamawa, Abba Jimetea ya bayyana hakan kwanan nan a wajen buda wata sabuwar hanya da Gwamnatin ta gina daga Girei-Wuro-Bokki. Abba Jimeta yace daukacin Mutanen Adamawa sun ce sai Atiku Abubakar.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya kashe Kasar nan
Abba Jimeta, wanda Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Adamawa, yace da zaran Alhaji Atiku Abubakar yace zai tsaya takarar Shugaban Kasa, to kowa a Jihar zai tashi tsaye wajen ganin an cika wannan buri. Abba Jimeta yace kaf Gwamnatin Adamawa tana bayan Atiku Abubakar.
Alhaji Atiku Abubakar, Turakin Adamawa ya rike Mataimakin Shugaban Kasar nan na shekaru takwas, lokacin Shugaba Obasanji. Mutanen Adamawa suka yayi abin a-zo-a-gani musamman a bangaren Tattalin arziki, Don haka suna bayan sa idan zai tsaya takara. Atiku Abubakar yana Garin Benin, wajen nadin sabon Gwamna, ba a sani ba ko zai tsaya takara ko ba zai tsaya ba.
Asali: Legit.ng