Zakuna Uku sun ceci karamar yarinyar aka sace a Ethopia
An saba samun labarin sace kananan yara a kasar Ethiopia, inda ake mika su ga maza don su aure su, sau tari idan aka yi ma yarinya haka a kasar, toh wahalar dasu akeyi da fyade da duka don su saba da zaman aure.
Hakan ya afku ga wata yarinya yar shekara 12, bayan an sace ta daga hannun iyayenta, inda aka gudu da ita can bayan gari. a wannan wuri ne wadanda suka sace ta suka dinga yi mata fyade.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewar ana cikin haka ne sai wasu Zakuna guda Uku inda suka yi wani gurnani daya sanya barayin yarinyar suka ranta ana kare, suka gudu suka bar yarinyar cikin daji.
KU KARANTA:Mace mai jarumta kamar Namiji
Nan fa Zakunan suka zagaye yarinyar da bata cikin hayyacinta, suka tsar eta har na tsawon awanni Uku, har sai da jami’an bada agajin gaggawa suka iso wajen, daga nan ne Zakunan suka koma cikin daji, aka wuce da yarinyar zuwa asibiti. Iyayen yarinyar da yansanda sun tabbatar da faruwar lamarin.
Jama’a na ganin wannan lamari a matsayin wani baiwa da Allah yayi ma yarinyar, ace Zaki dake cin mutum shine ke gadinta! Sai dai masana a fannin sanin halayyar dabba sunce wasu lokutta idan Zaki yaga karamin yaro na kuka, yana dauka cewa kukan dansa ne.
Toh! Koma dai menene, ita dai wannan yarinya ta samu tagomashi daga Zakuna.
Asali: Legit.ng