Kan wayar wuta ya caki kan Jariri

Kan wayar wuta ya caki kan Jariri

Wani jariri dan kasar Sin mai suna Chen Chen ya sha da kyar bayan ya fado a kan wayar wuta inda bakin wayar wutan ya shige cikin kashin kansa.

Kan wayar wuta ya caki kan Jariri

Rahotanni sun bayyana cewar Chen Chen ya fado kan wayar wutar ne a ranar Asabar 5 ga watan Nuwamba yayin da yake wasa a gidansu dake garin Guangzhou, kasar Sin.

Chen Chen na cikin wasa da kwallo a kan gadonsa, sai kwallon ta fadi kasa, garin ya dauko kwallon sai kawai ya fado kan wayar wutan, sanadiyyar haka bakin wayar wutar tayi ma kansa dameji.

KU KARANTA:Yayan Sanata Kabiru Marafa sun rasu sanadiyyar hadarin mota

Kan wayar wuta ya caki kan Jariri

Sai dai nan da nan aka garzaya da Chen Chen asibiti inda aka samu kwararrun likitoci suka yi masa tiyata har na tsawon awanni uku kafin aka samu nasarar cire karfen bakin wayar.

&index=41&list=PL6sEiOi0w1ZCJ2pYczvQeEWNY5u811xJt

Asali: Legit.ng

Online view pixel