Kungiyoyin Mafarauta na samun horo kan Boko Haram
- Za’a fara horar da yan banga a jihohin Adamawa da Taraba
- Yan sandan Najeriya sun gudanar da wani horon kwanaki biyar na musamman ga mambobi 251
- Horon zai bunkasa damar yan bindigan ta hanyar koya masu dabarun da ya dace.
A kokarin ganin an shawo kan mugun ayyukan yan ta’addan Boko Haram, hukumar yan sandan Najeriya ta gudanar da wani shiri na kwanaki biyar don bada horon da ya dace ga mambobin kungiyar yan biundiga daga jihohin Adamawa da Taraba.
KU KARANTA KUMA: Tinubu ya bar Najeriya ba saboda Oyegun ba
Kungiyar yan bindigan wadanda suka hada da mafaruta, wadanda suka taimakawa sojojin Najeriya kwarai da gaske gurin ci gaba da yaki da yan Boko Haram.
An shirya Horon na kwanaki biyar don ganin an taimakwa mafarauta yanda zasu inganta fasaharsu. A yayinda yake Magana da yan sandan dake Yola jihar Adamawa a ranar Laraba 9 ga watan Nuwamba, Murtala Aliyu kwamandan yan bindiga na jihar ya ce horon na da muhimmanci.
Aliyu yace horon zai inganta karfin yan bindigan ta hanyar samar da dabarun da suka dace domin su dada ba yan sanda da sauran hukumomin tsaro taimakon da ya dace gurin yaki da ta’addanci.
Kwamandan na jihar ya kuma bada shawaran cewa horon zai taimakwa mambobin nagarta a cikin yadda zasu gudanar da ayyukansu. Ya nuna jin dadinsa kan goyon bayan da mambobinsa suke samu daga al’umma a Adamawa.
KU KARANTA KUMA: Yan zanga-zanga sun mamaye Abuja kan zaben Rivers
Mista Aliyu ya yi alkawarin cewa yan kungiyarsa zasu ci gaba da bada gudunmuwarsu yanda ya dace domin bada tsaro a duk wani lungu da sako na kasar.
https://youtu.be/wXmmTEAKDxo
Asali: Legit.ng