Dangote ya bayyana dalilin karin kudin siminti

Dangote ya bayyana dalilin karin kudin siminti

- Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya tabbatar da cewa fasa bututun mai da tsagerun Niger Delta ke yi shi ya janyo tashin farashin siminti a kasuwanni.

- Ya ce rashin isasshen iskar gas sakamakon fasa bututu, shi ya tilasta kamfanin siminti na Dongote shigo da Kwal daga waje don samar da makamashi ga injinun kamfanin, lamarin da a cewarsa, ya kara yawan kudaden da ake kashewa wajen sarrafa Simintin.

Dangote ya bayyana dalilin karin kudin siminti
Cement bags

A wani labarin kuma, Rahotanni daga majalisar Dattawa sun nuna cewa sanatoci na nazarin yin watsi da sunayen jakadun wucin gadi su 46 da shugaba Muhammad Buhari ya gabatar masu don neman amincewarsu.

KU KARANTA: Karin kudin mai da NNPC yayi baiyi dai dai ba

Da yake karin haske kan batun, Mai Magana da yawun Majalisar, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce kwamitin majalisar kan Harkokin waje shi ya bayar da shawarar yin watsi da sunayen sakamakon korafe korafe da aka samu.

A wani labarin kuma, Rahotanni daga jihar Zamfara sun ce kusan mutane arba'in ne aka kashe a cikin wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai kan wata mahakar Zinari.

Haka ma wasu mutane da dama sun bata yayin da wasu suka tsira da munanan raunukka a cikin harin da aka kai ranar Litinin kan mahakar zinarin wadda ke daura da kauyen Bindim na karamar hukumar Maru.

Mazauna yankin sun shaida wa majiyar mu cewa harin ya zo bayan da 'yan bindigar wadanda ake zaton 'yan fashin shanu ne suka kwashe makonni suna satar mutane don neman kudin fansa.

"Yawancin wadanda suka mutun lebarori ne masu aikin hakar zinari da kuma wadanda suka zo saye." In ji wani mazauni yankin, kodayake kawo yanzu hukumomin tsaro a jihar ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

A wani labarin kuma Gwamnatin Najeriya na samarwa da rundunar sojojin ruwan kasar manyan jiragen yaki na zamani.

Yazu haka dai gwamnatin tarayya na ci gaba da mayar da hankali wajen samar da jiragen ruwan yaki ga rundunar ruwan sojojin Najeriya. A karo na biyu katafaren jirgin yakin da Najeriya ta sayo daga kasar China, ya isa kasar Angola kan hanyarsa ta zuwa Najeriya.

Daraktan watsa labarai a hedikwatar sojojin ruwan Najeriya, Komanda Christan Ezekobe, yace rundunar sojojin ruwan Najeriya suna ci gaba da samun manyan jiragen yaki irin na zamani da ake ji da su a wannan karni. Ya kuma ce jirgin farko ya isa Najeriya a bara, wannan kuma gashi yana kan hanya, wanda idan aka kaddamar da su zasu taka rawa sosai wajen samar da tsaro ta cikin ruwa.

Yanzu dai sojojin ruwan Najeriya zasu fara sintiri har zuwa gabar kotun Guinea. A cewar kwararre kan sha’anin tsaro Kwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa, aikin sojojin ruwa ne su kula duk wani abu dake faruwa ta cikin ruwa, wanda kuma ya hada da matsalar da ake samu a yankin Niger Delta inda ake fasa bututun mai ana kuma satar danyen Mai.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng