Shugaban kasa ya kaddamar da ayyuka a jihar Edo (Hoto)
A ziyarar aiki na kwana biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara a jiya zuwa jihar Edo, ya kai ziyarar ban girma tare da taya murna ga sabon Sarkin Bini Omo N’Oba N’Edo Uku Akpolokpolo Ewuare II a fadarsa.
Makasudin gudanar da ziyarar shine don kaddamar da wasu ayyukan da Gwamna Adams Oshiomole yayi.
Wasu daga cikin ayyukan da shugaban ya kaddamar sune: sabon babban Asibitin Bini, titin Siliko da suaransu. Shugaban ya samu rakiyar gwamna Oshiomole do kansa tare da zababben gwamnan jihar Godwin Obaseki zuwa wuraren kaddamar da ayyukan.
KU KARANTA: An garzaya da Maryam Ali zuwa Maiduguri
Gabanin isar shugaba Buhari jihar, sai da aka habbakla tsaro don tabbatar da ganin ya sauka lafiya, inda aka watsa jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, Sojoji, da yansanda a sassan jihar daban daban.
Wasu rahotanni sun nuna cewar ziyarar ta shugaban kasan ta sanya cunkoso akan hanyoyin garin, musamman hanyar titin siloko.
Ga wasu hotunan taron:
&index=38&list=PL6sEiOi0w1ZCJ2pYczvQeEWNY5u811xJt
Asali: Legit.ng