An garzaya da Maryam Ali zuwa Maiduguri

An garzaya da Maryam Ali zuwa Maiduguri

Wata majiya daga babban ofishin rundunar mayakan sojan sama ta bayyana cewa sun garzaya da daya daga cikin yan matan Chibok da aka kwato Maryam Ali Maiyanga zuwa garin Maiduguri a jirgi mai tashin angulu a ranar Litinin, 7 ga watan Nuwamba.

An garzaya da Maryam Ali zuwa Maiduguri

Idan za’a iya tunawa, da misalin karfe 6 na safiyar asabar 5 ga watan Nuwamba ne aka gano Maryam Ali yayin da Sojoji ke tantance mutanen da suka tsere daga dajin Sambisa a garin Polka, karamar hukumar Gwoza, inda daga nan ne aka garzaya da ita tare da yaron ta mai watanni 10 data same shit a hanyar aure da wani kwamandan kungiyar.

A ranar 14-15 na watan Afrilun shekara ta 2014 kungiyar Boko Harama ta sace yan mata 276 daga makarantar Chibok dake jihar Borno. Rahotanni sun bayyana cewa an aurar da Maryam ga wani kwamandan Boko Haram.

An garzaya da Maryam Ali zuwa Maiduguri

KU KARANTA:Mun ceto duk mutanen dake hannun Boko Haram - Buhari

Sai dai tun a baya an samu yan mata 57 da suka tsere daga hannun kungiyar, inda kuma kungiyar ta sako wasu 21 bayan wata yarjejeniya tsakaninsu da gwamnati. A yanzu haka jama’a na sa ran sauran matan ma zasu fito.

A watan Mayun 2016 ne aka gano daya daga cikin yan matan mai suna Amina, tace sauran matan na nan a hannun Boko Haram, amma fa 6 daga cikinsu sun rasu. Bayan sati daya ne aka sake gano daya daga cikin su, sai dai iyayen yan matan sun musanta cewa taa cikinsu, saboda babu sunan ta a jerin sunayen wadanda aka sace. Sai a watan Oktoban bana aka sako yan mata 21.

An garzaya da Maryam Ali zuwa Maiduguri

Wadannan sune kalubalen da gwamnati ke fuskanta, ana sa ran gwamnati na tattaunawa da yayan kungiyar don  sako sauran yan mata 83 da suka rage a hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel