Da Muhammad Abu Ali da sauransu sun tsere ma matuwa

Da Muhammad Abu Ali da sauransu sun tsere ma matuwa

- An kashe Laftanal kanal Ali da sauran sojoji a lokacin wani hari na ba zata da Boko Haram suka kai

- Da ace suna da kayyayin aiki na dare da sun dakatar da harin bazatar

- Har ila yau sojojin na shirin kai hari a dajin Sambisa

Cikakken bayanai sun zo kan yadda yan ta’addan Boko Haram suka kashe Laftanal Kanal Muhammd Abu Ali da sauran sojoji guda hudu.

Ya bayyana cewa babban jami’in baya cikin tankar lokacin da yan Boko Haram suka kai masu hari.

KU KARANTA KUMA: Ango Abdullahi ya zargi Buhari da rashin kishin arewa

 “Yana a wajen tankar; yana a waje tare da radiyonsa. Kuma saboda dare yayi, babu wanda ya ga ainahin makiyan da suka harbe shi.”

Da Muhammad Abu Ali da sauransu sun tsere ma matuwa
Laftanal kanal Abu Ali

 “Harbin yazo ta baya ne. lokacin da wadannan mutane (Boko Haram) suka zo, ya mika ta hanyar ne don ganin abunda ke faruwa. Baya cikin tankar.”

Ya kuma yi Magana game da mutuwar sojojin da za’a iya karewa inda ake akwai kayyayakin aikin dare.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokoki zata kama shugaban kwastam Hameed Ali

“Kun san, harin dare na da wahala a koda yaushe.”

 “Idan zaka je harin dare, dole kana bukatar abun ganin dare-madubin hangen nesa-saboda ka iya gane wanda ke kawo maka hari da kyau. Kun san hatsarin dake cikin yaki a cikin duhu? Rikicewa. Ba san wanene wanne ba.

 “Amman a fada maku wani abu, madubin hangen nesa guda biyu kawai bataliyan ke da shi. A wasu lokutan ma. Zaka samu bataliyan mutane basu da masu da madubin hangen nesa na dare ko daya.”

 “Ali yaje Mallam Fatori, kuma a lokacin da abubuwa ke tafiya daidai, sai bayan aikin ne wadannan yan Boko Haram din suka kai masu hari,” jami’in yaci gaba da bayani.

 “Sojojin na shirin kai wani hari dajin Sambisa, don haka ya kamata Ali ya janye daga Mallam Fatori saboda harin Sambisa. Yana shirin komawa ne lokacin da wannan abun ya faru.

Akwai shiri sosai, wanda ke nufin zai afku nan ba da daewa ba. Ya rigada ya samu umarnin janyewa daga Mallam Fatori ya kuma dawo Sambisa. Yana kuma nufin cewa da yan Boko Haram sun jinkirta kai harin na wasu yan kwanaki, da Ali ya bar Mallam Fatori a raye.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng