Soja 1 ya rasu wajen fada da ‘Yan Boko Haram

Soja 1 ya rasu wajen fada da ‘Yan Boko Haram

– Sojoji sun harbe wata ‘Yar kunar bakin wake na Boko Haram a Borno

An kashe wanna ‘Yar bakin wake ne a Garin Gwoza

– Sojan Najeriya Daya daga ciki ya rasa ran sa

Soja 1 ya rasu wajen fada da ‘Yan Boko Haram

 

 

 

Sojin Najeriya sun kara samun wata nasara a wajen yaki da ‘Yan Boko Haram, Sojojin sun gano wata ‘Yar kunar bakin wake na Boko Haram a Garin Gwoza da ke Borno, inda suka harbe ta har Lahira.  Kakakin Sojin Kasa, Kanal Sani Kukasheka ya tabbatar da haka a jiya.

Kanal Sani Kukasheka yace a Jiya, kimanin karfe 9: 45 na dare aka samu wata ‘yar kunar bakin wake za ta shiga Yankin da Sojoji suke a Kauyen Yamtake da ke Garin Gwoza, amma nan take wasu Sojojin kar-ta-kwana suka harbe ta, har lahira nan take. Bayan nan kuma Sojojin sun kara da ‘Yan Boko Haram a Yankin.

KU KARANTA: Masu gudu su gudu

‘Yan Boko Haram din sun kawowa Sojojin hari ne, amma ba su samu galaba ba. Sojojin Najeriya sun kashe ‘Yan Boko Haram din, sai dai Soji daya ya rasa ran sa. Rundunar Sojin ta samu karbe makamai na Bindigogin AK- 47 da harsashi da dama hannun ‘Yan ta’addan na Boko Haram.

Kwanakin baya, Premium Times ta rahoto cewa an harbe wani dan Boko Haram har lahira yayin da yake kokarin shiga sansani ‘Yan gudun Hijira watau IDP da ke Maiduguri. Bayan an gane sa, nan take aka shiga baza masa wuta har ya mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng