Yan zanga-zanga sun yiwa wata duka kan zargin kisan kai

Yan zanga-zanga sun yiwa wata duka kan zargin kisan kai

Wasu fusatattun yan zanga-zanga sun yiwa wata mata mugun duka bayan an zarge ta da kashe mijinta.

Wasu fusatattun yan zanga-zanga sun yiwa wata mai shekaru 45 Usha Devi wacce ta rasa mijinta kwanan nan duka bayan sun zargeta da kashe mijin nata da kanta.

Yan zanga-zanga sun yiwa wata duka kan zargin kisan kai
Yan zanga-zanga sunyiwa wata mai takaba duka kan zargin kisan kai

An bayyana cewa Devi wacce ta kasance matar gida ga Ashok Paswan ta jure wulakanci a hannun mijin nata kafin mutuwarsa. Lokacin da ya mutu a gidansu dake kauyen Samstipur a Bihar, kasar indiya, byan ta gama sha zagi, wasu kungiya na matasa gud 25 sun mamaye gidanta, suka tafi da ita gaban yaranta sannan sukayi mata mugun duka da sanduna har sai da ta rasa inda kanta yake.

Bayan an gama yiwa Devi duka a gaban daruruwan mutane dake kallo, an yasar da ita don ta mutu. Sai daga baya wani bawan Allah ya dauke ta zuwa asibitin Sadar inda aka magance mata raunukan da ta ji.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sace sakataren zabe na jihar Ekiti da dansa

Da aka kira mataimakin shugaban yan sandan Bihar, Tanveer Ahmed, ya bayyan a wannan:

“A yanzu haka muna nan muna bincikar al’amarin. Mun san cewa su biyun (mata da miji) sun samu sabani wanda ya zama tashin hankali babba. Ta buga wa mijinta sanda, sai yam utu. Muna jiran rahoton gwaji ne. matar na samun kulawa a asibiti a yanzu. Da zaran ta samu lafiya zamu ci gaba da bincike sannan mu gano abunda ya faru a nan kuma zamu dauki matakin da ya dace a kan matar da yan zanga-zangan idan bukatar hakan ta tashi."

Kalli wasu hotunan a kasa:

Yan zanga-zanga sun yiwa wata duka kan zargin kisan kai
Devi ta rafka wa mijinta sanda wanda yayi sanadiyar mutuwar sa
Yan zanga-zanga sun yiwa wata duka kan zargin kisan kai
Matasa 25 sun yiwa Devi dukan kawo wuka
Yan zanga-zanga sun yiwa wata duka kan zargin kisan kai
Ana ba Devi kulawa a asibiti

https://youtu.be/QBSX6fKoVc4

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng