Budurwa tayi kuka sakamakon yaudarar Samari

Budurwa tayi kuka sakamakon yaudarar Samari

Wata budurwa mai matsakaicin shekaru ta baiwa jama’a ma’abota shafin sadarwa na Facebook mamakoi bayan an gano ta tana ta rafka kuka tare da nuna bacin ranta saboda saurayinta yace ba ya yi.

Budurwa tayi kuka sakamakon yaudarar Samari

Ita dai wannan budurwa mai suna Gimbiya Chioma Mary ta daura hotunan tane yayin da take sharban kuka wii-wii a kafar sadarwa ta Facebook bayan saurayin da take tsananin kauna ya yaudareta, inda yace shi dai baya so, a kai kasuwa!

Wannan ne ya sanya Gimbiya Chioma ta kasa boye damuwarta, hart a kawo shi Facebook, sai dai dama Hausawa na cewa fahimta fuska, yayin da wasu suka tausaya mata, wasu kuwa sukan ta suka yi a Facebook din.

KU KARANTA: Buratai ya baiwa daliban jihar Nasarawa 150 gurbi a NDA

Gimbiya Chioma tace “sai da na bashi dukkanin makullan zuciyata ne zai min haka? Gaskiya nayi kuskure dana yarda dashi har cikin kokon zuciya ta”

Budurwa tayi kuka sakamakon yaudarar Samari

“Kada kuga laifina don nayi wannan rubutun, ya zaman min dole, kawata Nkechi, Shedrack ne fa ya yaudare ni. Abin bacin ran shi ne na bata lokaci na, an zage ni saboda shi, nayi makiya saboda shi, Nkechi na san zaki iya tuna abin da Ada ta min duk a kansa, don haka ki fada min dalilin da ba zan yi kuka ba.”

Hmmm, Soyayya gamon jini ce, amma inda kauna!

&list=PL6sEiOi0w1ZCJ2pYczvQeEWNY5u811xJt&index=46

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng