An dauki hoton wani fasto yana haurin wata mai ciki

An dauki hoton wani fasto yana haurin wata mai ciki

Ubangiji ya shirya fastocin wannan zamanin namu da kuma wani sanannen fasto a kasar Ghana, Daniel Obinim, wata na'urar daukar bidiyo ta dauke shi yana taka wata mace da nufin ze warakar da ita, bidiyon da aka dora a dandalin sadarwa na Instagram ya ja mutane da dama sunyi mummunan tsokaci kan yadda faston na cocin International God's Way church yayi haka.

An dauki hoton wani fasto yana haurin wata mai ciki

Bidiyon ya nuna faston yana magana a wasu yaruka na addu'a da nufin warkar da matar daga ciwo.

Obinim ya shiga cikin rudani na yin cewa shi ba faston gaskiya bane in da aka taba kaishi gaban kotu da aka caje shi da laifuka guda 7 a 2013, daga bi sani kuma kuma aka zarge shi da laifin kwanciya da matar wani karamin fasto a cocin su, wanda da baya ya amsa laifin sa yace amma ba matar karamin faston cocin su bane.

Ba dadewa ma an kama Obinim kan laifin dukan wasu masu zuwa cocin su a bainar jama'a kan laifin lalata da matan banza.

Wani yayi tsokaci inda yace" sakarai ko yesu be yi haka ba, in kana son yin wani abu daga Ubangiji to kayi mai addu'a.

Wani kuma yace wadan da suka yadda da shi ke bin wannan mahaukacin faston.

Asali: Legit.ng

Online view pixel