Yan bindigan Neja Delta sun fasa bututun man Trans Forcados
- Wasu yan bindigan Neja Delta sun fasa wata bututun man fetur wanda ya dawo aiki jim da kadan da gyara shi
- Wani hari ya faru ne bayan ganawar shugaba Buhari da shugabannin Neja Delta
Wata babbar bututun man fetur da ke garin warri ta sha wutan bam daga hannun yan bindigan Neja Delta a ranan talata ,1 ga watan Nuwamba, Punch ta bada rahoto.
Wata majiyar jami’an tsaro da shugaban unguwan sunce an fasa butun man ne awanni kadan bayan shugaba Buhar ya gana da shugabannin yankin Neja Delta domin tattauna matsalolin yankin.
KU KARANTA:Buratai ya baiwa daliban jihar Nasarawa 150 gurbi a NDA
Har yanzu dai babu kungiyar yan bindigan da suka dau alhakin harin.
Wani jami’in tsaro wanda aka sakaye sunan shu yace :@ “ an yi amfani da nakiya ne wajen kai harin kuma kwanan biyu kacal bayan an gyara bututun sakamakon fasa shi da sukayi kafin yanzu.”
Dickson Ogugu, shugaban unguwan Batan inda bututun yake ,ya tabbatar da faruwan kuma yace wata na’uran liken airi ta gano idan abun ya faru.
“Gaba daya man fetur ya shiga cikin Rafin da ke wurin yanzu, mune ke shan wahalan wallahi.”
Bututun kanfanin Pipelines and Product Marketing Company (PPMC) ce kuma ana turo mata mai ne daga Batan kusa da warri. Several militant groups, including the Niger Delta Avengers, have attacked oil facilities since February, reducing the nation’s output and hammering incomes.
Fasa bututun mai da yan bindigan yankin Neja Delta key i ya durkusar da tattalin arzikin Najeriya, shu yasa shugaba Buhari ya gana da shugabannin yankin domin shawo kan wannan abu, amma tsagerun sun babu ruwansu da ganawar da shugaba Buhari yayi da shugabannin.
Asali: Legit.ng