Gadar data hada jihohin Oyo da Kwara ta sake karyewa

Gadar data hada jihohin Oyo da Kwara ta sake karyewa

Matafiya masu bin hanyar Oyo zuwa Kwara sun shiga cikin firgici yayin da gadar data hada hanyoyin biyu ta karye karo na biyu a ranar Talata 1 ga watan Nuwamba.

Gadar data hada jihohin Oyo da Kwara ta sake karyewa

Gadar da akafi saninta da suna gadar Moro data hada titin Illorin-Igbeti ta karye, wanda hakan ya kassara hadadan kasuwancin al’ummar yankin.

Dan majalisa mai wakiltar al’ummar yankin Abdullahi Taiwo ya bayyana ma majalisar jihar Kwara faruwan lamarin a ranar laraba 2 ga watan Nuwamba, kwana daya da faruwar lamarin.

Taiwo yace karyewar gadar ya kawo tsaiko ga sufurin kayan amfanin gona da ake yi daga kayukan yankin zuwa garin Ilori. Daga nan sai ya bukaci a dauki matakin gaggawa don ganin an gyara gadar saboda muhimmancin da take da shi musamman ta bagaren shigowa da fitar da kayayyakin abinci ciki da wajen jihar Kwara.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban Kwastam ya mayar da fiye da Biliyan N1

Suma sauran yan majalisar da suka tofa albarkacin bakin su game da batun sun jaddada muhimmancin wannan gadar. Mataimakin Kaakakin majalisar Mathew Okadare ya umarci kwamitin kula da ayyuka da sufuri na jihar data hada kai da ma’aikatan ayyuka na tarayya don ganin an gyara gadar.

Majalisar tayi kira ga gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed daya samar da wata hanya da matafiya zasu cigaba da bi kafin kammala aikin gyaran gadar. Shima shugaban kula da ayyukan ma’aikatan ayyuka da sufuri na tarayya Omotayo Awosanya yace gwamnati ta shigar da aikin hanyar a cikin kasafin kudin bana, inda ma har ta yi tallar kwangilar.

Kazalika suma a jihar Legas, gwamnati na kokarin gina sabuwar gada ta hudu a jihar, sakamakon karuwan jama’a a jihar.

&index=47&list=PL6sEiOi0w1ZCJ2pYczvQeEWNY5u811xJt

Asali: Legit.ng

Online view pixel