Shugaba Buhari na ganawa a shugabannin yankin Neja-Delta
- Shugaba Muhammadu Buhari ya kasance yana baiwa yan yankin Neja Delta daman ganawa da shi
- Ganawar ta fara ne a misalin karfe 12 na ranan cikin fadar Aso Rock a da Abuja
A yanzu haka,Shugaba Muhammadu Buhari yana ganawa da masu ruwa da tsaki a yankin neja delta, jaridar Daily Trust ta bada rahoto.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kasance yana baiwa yan yankin Neja Delta daman ganawa da shi
Ana sa ran ganawar zata magance rigingimun da ke faruwa a yankin mai arzikin man fetur wanda ya durkusar da tattalin arzikin kasar.
KU KARANTA: Tashin hankali! An sace mutane 7 a makwannin biyu a wannan jihar ta Arewa
Ganawar ta fara ne a misalin karfe 12 na ranan cikin fadar Aso Rock a da Abuja.
Wadanda suke halarce a ganawar sune mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnati Babachir David Lawal,, Abba Kyari, da wasu ministoci da ma’aikatan gwamanati.
Masu ruwa da tsakin sun kunshi dattijo Edwin Clark, gwamnonin jihar Delta, Akwa Ibom, Bayelsa,Imo da kuma wasu manyan sarakan gargajiya a yankin.
Kana wasu shugabannin hukumomin tsaro na halarce a taron . an shirya taron ne domin tattaunawa akan kalubalen da ya shafi yankin da kuma hanyoyin da gwamnati za ta iya amfani da shi wajen magance wadanan kalubale.
Asali: Legit.ng