Yan luwadi sun shiga hannu a Kano

Yan luwadi sun shiga hannu a Kano

Mutane sun cika da mamaki bayan an kama wasu mutane su biyu turmi da tabarya suna luwadi da wani karamin yaro mai shekaru 10 da tsakar rana.

Yan luwadi sun shiga hannu a Kano

Jaridar The Cables ta ruwaito an gurfanar da Labaran Abdullahi mai shekaru 25 da Sani Umar mai shekaru 35 mazauna unguwar Tudun Rubudi dake Kurnan Asabe gaban kotun majistri a ranar 28 ga watan Oktoba kan zarginsu da aikata laifin fyade na luwadi ga wani karamin yaro.

Wani makwabcinsu mai suna Sageer Muhammad tare da yan bangan unguwar Bachirawa ne suka kama su da misalin karfe 11 na dare suna aikata danyen aikin ga karamin yaron.

KU KARANTA: Duba abin mamakin da aka gani a Abuja (Hotuna)

Lauya mai kara yace daga nan ne aka garzaya da karamin yaron zuwa asibitin tunawa da Waziri Shehu Gidado don duba lafiyarsa. Lauyan yace laifin da ake zargin mutanen da aikatawa ya saba ma sashi na 284 da na 183 na kundin hukunta laifuka.

Ana tuhumar su da aikata sabo da cutar da mutane, sai dai mutanen sun ki amsa laifukansu. Amma alkalin kotun majistri Ibraheem Khaleel ya umarci da a dauresu a gidan kaso, har sai ranar 29 ga watan Nuwamba da za’a cigaba da sauraron karar.

A nan sai dai muce, Allah yasa mufi karfin zuciyar mu.

&list=PL6sEiOi0w1ZCJ2pYczvQeEWNY5u811xJt&index=96

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: