Wata Amarya ta ruga a guje yayin da za a daura mata aure
- A jihar Delta Wata Amarya ta ruga a guje yayin da ske shirin daura mata aure
- Wannan Amarya ta ce ba tayi, ana tsakiyar taro
- An ga Angon ta a guje yana bin ta a baya, yana ba ta hakuri
A jihar Delta wani abin mamaki da al’aji ya faru a wannan makon. DailyPost ta rahoto cewa an dakatar da wani daurin aure bayan da Amarya ta sheka a guje ta bar wurin bikin. Wannan Amarya ta ce ita fa sam ta fasa yin auren.
Bayan ta ruga, can aka hangi Angon ta a baya yana gudu, domin ya shawo kan ta, ya ba ta hakuri. Wannan abu dai ya faru ne a Garin Udu da ke Jihar Delta. Mutane ne dai sun tsaya kallon sarautar Ubangiji, inda suka ga Ango ya bi kan titin Orhunworhun a guje yana neman Amarya ta dawo a daura masu aure.
Ana dai cikin tsakiyar biki, wannan Amarya ta arce a guje ta bar dakin taron, tace fau-fau ta kuma fasa auren. Sai dai har yanzu ba a san menene ya faru, ya jawo hakan ba. Amma dai wannan abu ya ba jama’a mamaki kwarai.
A wata Kasa kuwa wata mata ta haifi wani yaro mai kafafu barkatai guda hudu, yanzu haka ana ta kokarin yi wa wannan yaro aiki domin ceto ran sa. Wannan abin al’ajabi ya faru ne a Kasar Mozambique.
Asali: Legit.ng