Mutane 6 da suke rike da madafan iko a Najeriya
- Ana ta kukan cewa wasu mutane sun rike madafan iko a gwamnatin Baba Buhari
- Ko su wanene wadannan mutane da ba a san su ba?
- Kwanaki dai har sai dai matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta koka a BBC
A wancan karo mun kawo jerin wasu mutane da ake tunanin sune suka rike madafan iko a Kasar nan. A yau mun karasa kawo ragowar mutane uku kamar yadda muka yi alkawari.
Wasu ministoci
Wasu daga cikin Ministocin Gwamnatin sun zama masu fada a ji a Gwamnatin Buhari da kuma Jam’iyyar su ta APC. Wadannan Ministoci da suke da ta cewa a Majalisar zartarwar Tarayya kuwa sune Tsohon Gwamnan Legas da na Rivers; Babatunde Raji Fashola daRotimi Amaechi, watau Ministan Sufuri da kuma Ministan Wuta, Muhalli da Ayyuka na Kasar.
KU KARANTA: Kaji wadanda suke rike da madafan iko a Gwamnatin Najeriya
Isma’il Funtua
Ko da yake ba kowa ne ya ma taba jin sunan wannan mutumi ba, amma kamar Mamman Daura yana daga cikin mutanen da suke rike da madafan iko a Kasar nan. Isma’il Funtua, aminin Buhari ne yana kuma da ta cewa a tafiyar Gwamnati; yana cikin masu fadawa Shugaba Buhari wadanda za ya nada a Gwamnatin sa
TY Danjuma
Theophilus Yakubu Danjuma, wanda yana cikin manyan Kasar nan. TY Danjuma mai gidan Shugaba Buhari ne tun a Soja da kuma Gwamnati, har yau kuma yana girmama sa. TY dajuma tsohon Janar ne, yana cikin wanda suka yi wa Shugaba Buhari yakin cin zabe. TY Danjuma yayi sanadiyar nada wasu Ministoci da masu manyan mukamai cikin Gwamnatin Buhari.
[karashe daga kashi na farko]
Asali: Legit.ng