Rahama ta fara shirin fim tare da Akon
Tsohuwar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta fara aiki a shikin shirin ‘The America King’ tare da shahararen mawaki, Akon da sauran jaruman fim.
A farkon wannan satin ne jarumar wacce ta fito a shirin wasa tare da darakta wanda ya amshi lambar yabo, Jeta Amata ta yada hotunan wasan da suke shiryawa a shafinta na zumunta tare da masoyanta.
Tace: “Kuna da daraja kuma baza’a iya canza kuba, idon wani ya taba fada maku akasin haka, karda ku yarda da hakan. Kawai kuyi kokari ku kasance kanku ko sau daya ne.”
Anyi shirin wasan ne a Los California ya kuma samu soyayyar jarumai irin su Enyina Nwigwe.
KU KARANTA KUMA: Anyiwa yar Buhari ba’a kamar yadda ta zama mata ta 4
An kori jarumar daga wasa a kamfanin Kannywood ne, bayan ta fito a cikin wani bidiyon waka tare da ClassicQ wanda aka zarge ta da rungumar mawakin.
Kungiyar masu ruwa da tsaki na MOPPAN ne suka kaddamar da takardan korar jarumar, bisa ga hujjar cewa abunda tayi ya saba ma kundun tsarin kungiyar, harma suka ce koda wani jarumin daban ya aikata irin abunda tayi, babu shakka doka zatayi aiki a kansa.
bayan dakatarwan tata ne shararen mawakin nan na kasar Amurka, Akon ya mika tayinsa gareta, inda ya gayyaceta zuwa Hollywood domin ta shiga cikin shirin wasar su.
https://youtu.be/-djNyHh_-y4
Asali: Legit.ng