An zaftare farashin wayar salula a Kasar Ghana
- Ma’aikatar sadarwa ta ba Kamfanun wayar salula umarnin su rage farashin kudin wayar salula a Kasar Ghana
- Haka kuma an rage kudin shigo da wayar salula cikin Kasar
- Sai dai a Najeriya, ana kokarin kara kudin wayar ne
Makwabciyar Najeriya, Ghana ta rage kudin wayar salula a Kasar.
A kasar Ghana an zaftare farashin kudin wayar salula da kashi 10%. Gwamnatin Kasar ta ba Kamfunan kera wayoyin salula da su rage farashin wayoyin na su domin yayi daidai da farashin kasuwar Kasar.
Mutanen Kasar dai sun koka kwarai bayan da Gwamnati ta kara farashin wayoyin a shekarar bara, Gwamnatin Kasar ta kara kudin wayoyin da ake shigowa da su Kasar da kashi 10% don ya zama daidai da tsarin farashin ECOWAS watau CET.
KU KARANTA: Za a hana bara a Najeriya
Har wa yau dai Gwamnatin Kasar Ghana ta cire harajin da ke cikin shigowa da wayar salula Kasar. Sai dai a Najeriya sam abin ba haka yake ba, Majalisar Tarayyar Kasar na kokarin shigo da wani karin haraji na kaso 9% na duk abin da aka kashe a wayar salula. ‘Yan Kasar dai sun koka da wannan yunkuri.
Kwaku Sakyi Addo, wanda shine Shugaban Ma’ikatar sadarwa ta wayar salula na Kasar Ghana ya bayyanawa Gidan Talabijin Citi Business News cewa Gwamnatin Kasar na kokarin ganin wayar salula sun yi araha, har ace kowane irin talaka zai iya mallakar wayar. Gwamnatin Kasar ta kira masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa su bi wannan umarni.
Asali: Legit.ng