Za tayi shekaru kusan 100 a gidan yari saboda zamba

Za tayi shekaru kusan 100 a gidan yari saboda zamba

- An yankewa wata mata ‘yar Enugu hukuncin shekaru 90 a gidan yari bayan an kama ta da laifi

- Hukumar EFCC ta kai karar Miss Chika Amsy Charles bisa zargin laifuffuka akalla 30

- Yanzu wannan mata za tayi shekaru 90 a gidan yari bayan ta tabbata ta yaudari wasu mutane

Za tayi shekaru kusan 100 a gidan yari saboda zamba
Chika Amsy Charles

 

 

 

 

 

Wani Kotu a jihar Enugu ya yankewa wata mata hukuncin shekaru 90 a Gidan Yari bayan an kama ta da laifin zamba. Wannan mata Chika Amsy Charles ta cuci wasu yara kudi har Miliyan 5.6 da sunan za ta sama masu makaranta ta wani Kamfanin ta na bogi.

Chika Amsy Charles ta cuci wasu yara har uku cewa za ta shigar da su Jami’ar fasaha ta Jihar Enugu. Daya daga cikin wadannan yara ya kai kara Hukumar EFCC, wannan abu ya faru ne tun a shekarar 2007. Yanzu haka dai, Babban Kotun Tarayya na Kasar da ke Enugu ta yankewa wannan mata daurin shekaru 90 a Gidan Yari.

KU KARANTA: Wani yayi wa Dan Sanda shegen duka

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa wani Babban Kotun Tarayya na Kasar da ke zaune a Kaduna ya yankewa wani Tsohon akawun Karamar Hukumar Giwa da ke Jihar. Kotu ta samu Amina Ya’u da laifin satar kudi, an yankewa wannan mutumi shekara biyar a gidan yari.

A wani labarin kuma Hukumar EFCC ta bada belin mai magana da bakin Tsohon Shugaban Kasa, Dr. Reuben Abati ya sha tsari na kwana 3, Hukumar EFCC ta kama Abati a Ranar Litinin din nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng