An gano Jamila Tangaza na shirin tserewa

An gano Jamila Tangaza na shirin tserewa

- Hukumar jami'an fararen kaya (DSS) ta kama wani matashi mai suna Idris bisa zarginsa da yunkurin kitsawa tsohuwar ma'aikaciyar BBC, Jamila Tangaza yadda za ta gudu ta bar kasar ta wata karamar boda a jihar Kwara

- Hukumar ta kama matashin ne dauke da fasfo din Jamila Tangaza a lokacin da hukumar shige da fice na kasa dake yankin Chikanda a jihar Kwara ke kokarin mannawa fasfo din sitam

An gano Jamila Tangaza na shirin tserewa
Jamilah Tangaza

Kamar yadda hukumar ta DSS ta bayyana, Jamila Tangaza na jiran ta karbi fasfo din ne don ganin ta bar kasar ta wannan bodar. Kuma har zuwa yanzu ba a gan ta ba bayan matashin ya sanar da ita halin da yake ciki.

A cikin watan Agusta ne dai hukumar EFCC ta kama Jamila Tangaza bisa zarginta da wawure naira milyan 800 a lokacin da take rike da mukamin darakta na ma'aikatar AGIS da kuma mukamin babbar mai taimakawa tsohon ministan Abuja, Sanata Bala Mohammed.

Wata majiya daga hukumar EFCC ta bayyanawa majiyarmu ta Sahara Repoters cewa ta yi mamakin yadda Tangaza ta sake samun wani fasfo din duk da cewa ta ajiye fasfo dinta na ainihi a ofishin hukumar a lokacin bada belinta.

Majiyar ta kara da cewa za a sake kama Tangaza tare da tsohon ministan Abuja da zarar an kammala bincike.

Tuni dai hukumar ta EFCC ta garkame tsohon ministan na Abuja, Sanata Bala Mohammed a ofishinta bisa zarginsa da salwantar da wasu bilyoyin kudade a daren jiya Litinin.

A wani labarin mai kama da wannan kuma, Tsohon ministan jiragen sama, Femi Fani Kayode ya yanke jiki ya fadi a komar hukumar EFCC dake Abuja a ranar Asabar din da ta gabata, kamar yadda tsohon dogarinsa, Jude Ndukwe ya bayyanawa manema labarai a jiya Litinin.

Jude ya kara da cewa ba dan daukin gaggawar da jami'an lafiya na hukumar suka kawowa Fani Kayode ba, da labari ya sha bamban.

https://youtu.be/_NPmiLLH9JU

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel